Makomar Kano Pillars da Katsina United na hannun juna ranar Alhamis

0
96

Makomar ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa masu tsananin hamayya da juna a, Kano Pillars da Katsina United, na hannun junansu a yunƙurin komawa gasar Firimiyar Najeriya ta NPFL da suke yi.

Pillars za ta fafata da Katsina ne a ranar Alhamis a wasan ƙarshe na cikin Rukunin Arewa a gasar Nigeria National League (NNL) a garin Asaba na Jihar Delta.

Pillars ce ke saman teburin da maki shida, yayin da Katsina ke biye mata da maki uku. Sai kuma EFCC FC mai maki 1 da kuma DMD FC maras maki.

Duk wanda ya yi nasara tsakanin abokan hamayyar shi ne zai buga wasan ƙarshe da ƙungiyar da ta lashe Rukunin Kudu, wanda Sporting Lagos ke jan ragama da maki shida, Heartland mai maki huɗu, Stormers SC mai ɗaya, sai FC One Rocket maras maki.

Saɓanin rahotannin da aka dinga yaɗawa tun ranar Litinin cewa Pillars ta samu gurbin NPFL, dole ne sai ta samu aƙalla maki ɗaya nan gaba ko kuma idan ta yi rashin nasara a hannun Katsina to ya kasance ƙwallayen da aka zira mata ba su kai huɗu ba.

A yanzu Pillars na da ƙwallo uku da ta zira a raga cikin wasa biyu, yayin da Katsina ta ci uku kuma aka zira mata uku – ba ta da ƙwallo ko ɗaya ke nan a yanzu.

Jim kaɗan bayan tashi daga wasan wasu magoya baya suka fara taya Pillars murnar cewa sun haura gasar NPFL a shafukan sada zumunta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here