Alhazan Najeriya na fargabar komawa Madina

0
99

Alhazan Najeriya sun shiga damuwa bisa samun labarin akwai yiyuwar su sake komawa Madina a lokacin da za su koma gida.

Aminiya ta rawaito cewa hukumomin  Saudiyya sun shaidawa Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) cewa tashar jiragen Sarki Abdulazeez da ke Jidda ta cushe don haka dole jiragen da ke jigilar alhazan Najeriya su yi amfani da tashar Madina.

Abinda ya tayar da hankalin alhazan shi ne tafiyar awa bakwai zuwa takwas dake tsakanin Makka da Madani saɓanin awa ɗaya kacal dake tsakanin Makka da Jidda.

Alhazai da dama da Aminiya ta zanta da su sun roƙi gwamnatin Saudiyya ta janye wannan tsarin duba da cewa zai iya cutar da lafiyarsu.

Wata mai ciwon ƙafa, Hajiya Hauwa Muhammad ta ce wannan tafiyar za ta wahalar da ita.

Ta ce “Irinmu masu fama da ciwon ƙafa muna cikin damuwa ƙwarai da gaske domin mutum ya zauna ya yi awa takwas a  mota sannan ya shiga jirgi ya kwashi wasu awannin,  kin ga akwai damuwa”

Shi ma wani dattijo Alhaji Isah Ado ya yi kira ga hukumomin Najeriya da su yi ƙoƙarin shawo kan lamarin cikin gaggawa.

A na sa ɓangaren, shugaban Hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Kano,  Alhaji Lamin Rabiu Danbappa ya tabbatar da wannan magana amma ya ce NAHCON na tattaunawa da hukumomin Saudiyya domin su janye wannan tsarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here