An samu raguwar hatsarin ababen hawa yayin Babbar Sallar bana – FRSC

0
141

Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) ta ce an samu raguwar yawan hatsarin motar da ake fuskanta a yayin Babbar Sallar bana.

Hukumar ta kuma ce hakan na nufin an samu rangwame hatta a yawan hatsarin da kuma adadin wadanda ke mutuwa ko jin rauni idan aka yi hatsari.

FRSC ta ce yayin bukukuwan da aka kammala a kwanan nan, yawan haduran sun ragu da kimanin kaso 25 cikin 100, sai jin rauni da kaso 43, yayin da mace-mace ya ragu da kaso 53.

A cikin watan sanarwa da Kakakin hukumar na kasa, Bisi Kazeem ya fitar ranar Laraba, ya alakanta nasarar da sabon salon da hukumarsu ta dauka wajen wayar da kan masu tuki.

A cewar sanarwar, sabanin mutum 88 da suka mutu da 373 da suka jikkata a Babbar Sallar bara, a bana mutum 38 ne suka rasu, 211 kuma suka jikkata.

Ya kuma ce hukumar ta tattara yawan laifukan da aka aikata da suka kai 4,682 a hanyoyi 2,053 a tsakanin lokacin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here