Gwamnan Kano ya dibar wa kwamishinoninsa wa’adin sake tantance su

0
217
Abba Gida-Gida
Abba Gida-Gida

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya tabbatar wa kwamishinonsa cewa za a tantance su bayan wata shida da kama aiki domin sanin waɗanda za su ci gaba da aiki da kuma waɗanda za a kora.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da majalisar zartarwar jihar ta yi zamanta na farko a yau Laraba.

A cikin jawabin da ya gabatar, Abba ya ce “Ina tunatar da ku cewa kuna da wata shida na gwaji bayan naɗa ku kan muƙami, bayan haka ne za a duba ayyukan da kowace ma’aikata ta gudanar, za a yaba wa waɗanda suka yi ƙoƙari sannan za a yi waje da waɗanda ba su yi ƙoƙari ba.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here