Jihohi 14 da za su fuskanci ambaliyar ruwa — NEMA

0
155

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta zayyana jihohi 14 da yankuna 31 da ka iya fuskantar mamakon ruwan sama mai karfin gaske wanda zai iya haifar da ambaliya daga ranar 4 zuwa 8 ga watan Yuli.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mista Ibrahim Farinloye, Kodinetan NEMA, da me ofishin hukunar a jihar Legas.

Farinloye ya bukaci masu ruwa da tsaki a jihohin da abin ya shafa da su dauki matakan kariya domin dakile asarar rayuka da dukiyoyi.

Ya lissafa jihohin da yankunan kamar haka:

Filato: Langtang da Shendam

Kano: Sumaila da Tudun Wada

Sakkwato: Shagari, Goronyo da Silame

Delta: Okwe

Kaduna: Kachia

Akwa Ibom: Upenekang

Adamawa: Mubi, Demsa, Song, Mayo-belwa, Jimeta da Yola

Katsina: Katsina, Jibia, Kaita da Bindawa

Kebbi: Wara, Yelwa da Gwandu

Zamfara: Shinkafi da Gummi

Borno: Briyel

Jigawa: Gwaram

Kwara: Jebba

Neja: Mashegu da Kontagora

Farinloye ya gode wa Hukumar Hasashen Ruwan Sama (FEWS) da Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya Abuja bisa bayyana bayanan daminar bana akan lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here