Babbar Kotun tarayya ta dakatar da yunkurin gayyatar Ganduje kan bidiyon dala

0
88

Babbar kotun tarayya dake zamanta a Kano karkashin jagorancin Justice A M Liman ta dakatar da hukumar karbar korafe korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta kano da sauran hukumomin tsaro daga gayyata ko kama tsohon Gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Wannan na kunshe ne cikin wata dakatarwa ta wucin gadi da kotun tayi har sai ta saurari karar dake gabanta data shafi zargin take hakkin Dan Adam da tsohon Gwamna Ganduje yashigar.

Kotun dai ta sanya ranar 14 ga watan Yuli amatsayin ranar da zata fara sauraron karar.

Hukumar ta PCACC dai ta aikawa tsohon Gwamnan da takardar gayyata domin amsa tambayoyi kan wani fefan Bidiyo da ake zargin Dr Ganduje na karbar kudaden kasashen waje, duk kuwa da cewa yasha musantawa.

A ranar alhamis data gabata, bayan bullar waccen gayyata, Jam’iyyar APC mai hamayya a Kano ta fitar da wata sanarwa inda take kira ga tsohon Gwamnan da yayi watsi da waccen gayyata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here