Tinubu ya bude shafi a sabuwar manhajar Threads kishiyar Twitter

0
109

Shugaba Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya shiga ayarin dubban mutanen da suka bude shafi a sabuwar manhajar Threads kishiyar Twitter.

Mashahurin Mai kudin nan kuma mamallakin kamfanin Meta, Mark Zuckerberg, ne ya ƙaddamar da Zaren don yin gasa da Elon Musk mai kamfanin Twitter.

Meta ya ce sama da mutane miliyan 30 ne suka yi rajistar bude sabon shafin na Threads zuwa wannan lokaci.

Shugaba Tinubu ya wallafa rubutunsa na farko kan Threads kamar sauran mabiya sabuwar manhajar.

Fitattun ‘yan Nijeriya, wadanda suka yi rajistar a manhajar sun hada da mawaka da ‘Yan fim da dai sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here