Kona Qur’ani: Houthi ta hana shiga da kayan Sweden cikin Yemen

0
113

Ƙungiyar ‘yan Shia ta Houthi da ke iko da arewacin Yemen ta ce ta hana shigar da kayan da aka sarrafa a Sweden don nuna ɓacin ranta da ƙona Ƙur’ani mai tsarki da aka yi a ƙasar. 

Gidan talabijin da Houthi ke gudanarwa na Al Masirah TV ya ruwaito ministan kasuwanci na ƙungiyar yana cewa su ne ƙasar Musulmi ta farko da ta ɗauki irin wannan mataki. 

Duk da ya ce kayan Sweden “ba su da yawa”, ya bayyana matakin da “na musamman” kuma ya nuna “irin abin da Houthi ke iya yi”. 

Ya kuma yi kira ga ƙasashen Musulmai da su bi sawunsu. 

A ranar jajiberin Babbar Sallah ne wani mutum ya ƙona Ƙur’anin a wajen wani masallaci na birnin Stockholm bisa kariyar ‘yan sanda, yana mai cewa ya yi ne don ya nuna ‘yancinsa na faɗar albarkacin baki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here