PSG ta ɓullo wa Mbappe ta bayan gida, Inter Milan na son Lloris

0
111

Kylian Mbappe na ganin kila zai bar Paris St-Germain a bazarar nan saboda ba shi da niyyar tsawaita kwantiraginsa a kungiyar ya wuce shekara mai zuwa 2024 kuma zabinsa shi ne ya tafi Real Madrid. (ESPN)

Sai dai kuma PSG wadda ta yi amanna cewa tuni Mbappe ya zabi ya koma Real Madrid a kyauta a bazara mai zuwa, ta nuna cewa idan har ya ki ya sanya hannu a wata sabuwar yarjejeniya da ita, to ba shakka za ta sayar da shi ga duk kungiyar da ta iya biyan farashin da ta sanya masa a wannan bazarar. (Sky Sports)

Kungiyar farko da Mbappe zai fi so idan da gasar Premier zai koma da ita ce Arsenal, to amma kuma farashinsa ya fi karfin Gunners din kuma ma ba wata ganawa da aka yi tsakaninsa da kungiyar ta Landan. (Independent)

Newcastle United na fatan kammala cinikin dan wasan gaba na gefe na Leicester City Harvey Barnes a kan fam miliyan 35, kafin Aston Villa da West Ham su yi mata shigar sauri a kan dan tawagar ta Ingila. (Guardian)

Dan gaban Portugal Joao Felix na matukar son tafiya PSG to amma kuma karshenta ya ci gaba da zama a Atletico Madrid, wadda ke son yuro miliyan 100 a kan dan wasan mai shekara 23. (AS )

Inter Milan na kara himma a zawarcin da take yi na golan Tottenham Hugo Lloris, mai shekara 36, domin ya maye mata gurbin Andre Onana, wanda zai tafi Manchester United. (Foot Mercato)

Borussia Dortmund na sa ido a kan tsohon dan wasanta na gaba na gefe Jadon Sancho a Manchester United, ko da yake ana ganin yana son ci gaba da zama a Old Trafford. (Sky Sports)

Sporting Lisbon ta amince ta sayi dan gaban Coventry City Viktor Gyokeres dan Sweden mai shekara 25 a kan yuro miliyan 24 . (Fabrizio Romano)

Kociyan Atletico Madrid Diego Simeone zai yi watsi da tayi mai tsoka da kungiyar Al Ahli ta Saudiyya ta yi masa, saboda ya fi son ci gaba da zama a kungiyar ta Sifaniya. (ESPN)

Watakila Mason Greenwood ya kawo karshen kauracewar da ya yi wa wasan kwallon kafa ta wata 18, domin kungiyar Atalanta na sha’awar aron dan wasan na gaba na Manchester, mai shekara 21. (Mirror)

Dele Alli ya koma atisaye da Everton a kokarin da yake yi na farfado da wasansa, yayin da kociyan kungiyar Sean Dyche ya fada masa cewa yana bukatar ya dawo kan ganiyarsa. (Mail)

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta bai wa Lee Carsley sabon kwantiragi domin ya ci gaba da aikin horda da tawagar kasar ta ‘yan kasa da shekara 21 bayan da ya jagorance ta zuwa wasan karshe na duniya. (Mail)

John Terry ya ce ya koma tsohuwar kungiyarsa Chelsea inda yake aiki da cibiyar renon ‘yan wasan Stamford Bridge din. (John Terry)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here