Wata hajiya ‘yar Najeriya ta mayar da kudi Dala 80,000 da ta tsinta a kasar Saudiyya

0
130

Wata hajiya yar Najeriya daga jihar Zamfara, Aishatu y’an Guru Nahuce ta mayar da kudi kimanin dalar Amurka 80,000 da ta tsinta a kasar Saudiyya.

Mahajjaciyar wadda ta fito daga karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara ta tsinci kuɗine wanda a kuɗin Nigeria ya Kai kimanin (N56,000,000), kuma ta mika kudin ga jami’in hukumar jin dadin alhazai ta Zamfara domin mayar da kudin ga masu su .

A halin yanzu dai ana ta yabawa Hajiyar Saboda hali na kwarai da ta nuna.

Al’umma da dana suna ta tsokaci akan lamarin, musamman a dandalin sada zumunta na Facebook da Twitter.

Da yake tsokaci a kan sakon, wani Isa Abba Kyari ya ce, “Allah cikin rahamarsa marar iyaka ya sakawa Hajiyar da alkhairi . Haka kuma gwamnatin jihar Zamfara ta yi mata kyauta ta musamman, domin karfafa gwiwar sauran al’umma don su yi koyi da ita.”

Wani Kayode Festus Abdulgafar ya ce, “Ya kamata gwamnatin Najeriya ta baiwa wannan babbar jakada ta kasa lambar yabo idan ta dawo gida. Kuma Ina fatan Allah Ta’ala Ya Saka mata da alkhairi”.

Sani Suleiman ya ce, “Allahu akbar, wannan babban rabo ne a gare ta da iyalanta, Allah ya Saka mata da alkhairi, ya kar6i Hajjinta”.

Chiri Sarki ya rubuta cewa, “Hukumar kula da aikin hajji ta Nigeria ya kamata ta yabawa matar domin ta yi abun da ya fito da kimar Nigeria a idon duniya.

Sai dai wasu sun nuna damuwa kan dimbin makudan kudaden da aka ce an Yar har matar ta tsinta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here