Wasu kungiyoyin fararen hula sun rubuta takardar koke ga Amurka da Tarayyar Turai suna neman su hana gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf izinin shiga kasashensu.
Sun kuma ce sun rubuta makamancin wannan korafin ga China da sauran kasashe.
Kungiyoyin, wadanda ke karkashin inuwar Gamayyar Samar da Shugabanci Nagari (CGGCI) sun ce sun yi kiran ne saboda abin da suka kira yawan rushe-rushen da Gwamnan ke yi tun da ya hau mulkin Jihar.
A wata takardar korafi da Shugaban Kungiyar na kasa, Kwamared Okpokwu Ogenyi, ya sanya wa hannu, kungiyar ta bukaci a hana Gwamnan da iyalansa da kuma shugabanni da mambobin jam’iyyarsa ta NNPP izinin saboda abin da suka kir take hakkin dan Adam da sunan rusau.
Kwafin takardar korafin dai da aka raba wa manema labarai ranar Asabar, ya yi zargin cewa yayin rusau din, an yi asarar rayuka da na dukiyar sama da Naira biliyan 200.
Kungiyoyin sun kuma yi zargin cewa da gangan Gwamnan yake rusau din saboda ya goge duk ayyukan alherin da tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi lokacin da yake mulkin Jihar.
“A kan haka ne muke so a hana shi, tare da dukkan Shugabannin jam’iyyarsa ta NNPP a matakin Jihar da ma kasa baki daya, izinin shiga kasashen. A halin yanzu, wannan ne kawai abin da za a yi masa don ya shiga taitayinsa,” in ji kungiyoyin.