Yadda za ku nemi agajin gaggawa da sabuwar manhajar ‘yan sanda

0
184
Police, Nigeria

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta fitar da sabuwar manhaja wadda mutane za su iya amfani da ita domin neman agajin gaggawa.

Babban Sufeton ‘Yan sandan Nijeriya Olukayode Egbetokun a ranar Asabar ya bukaci ‘yan kasar su sauke sabuwar manhajar a wayoyinsu da kuma amfani da ita idan bukata ta taso.

Manhajar, mai suna “NPF Rescue Me”, an tsara ta ne domin sanar da ‘yan sanda wani lamari da ke faruwa da kuma bukatar agajin gaggawa.

Mutum zai iya bayar da rahoton wani laifi ko wani abu da ke faruwa, sannan za a iya kai karar dan sanda idan ya yi kuskure.

Haka kuma za a iya sanar da ‘yan sanda domin turo motar daukar marasa lafiya idan an samu hatsari ko kuma mara lafiya na bukatar agajin gaggawa.

Sa’annan za a iya kiran sashen ko-ta-kwana na ‘yan sanda domin magana da su kai-tsaye.

Ga hanyoyin da za ku bi domin sauke manhajar da kuma yin rajista.

– Da farko dai masu wayar Android za su je Playstore, su kuma masu amfani da IOS su je Appstore domin sauke manhajar NPF Rescue Me.

– Bayan kun sauke manhajar, sai ku shiga ciki domin yin rajista.

– Da zarar an shiga cikin manhajar, za a bukaci mutum ya saka adireshinsa na imel, bayan haka za a turo maka wasu lambobi na sirri guda hudu nan take ta adireshinka na imel.

– Sai ka shiga imel dinka ka kwafo wadannan lambobi na sirri sa’annan ka rubuta su a gurbin da aka tanada a cikin manhajar. Ko da ba a turo maka lambobin ba akwai gurbi daga kasa wanda za ka iya bukatar a sake turo maka lambar.

– Daga nan kuma sai yin rajista inda za ka cike guraben da aka tanada.

– Ana bukatar mutum ya saka sunansa da na mahaifinsa da ranar haihuwa da adireshin gida da jihar da mutum yake zama da aikinsa da adireshin wurin aiki. Sa’annan daga can sama akwai gurbin wurin da mutum zai saka hotonsa – tilas ne a saka hoto.

– Sai kuma gurbin da mutum zai saka sunan asibitin da yake zuwa da rukunin jininsa da kuma wasu bayanai game da lafiyarsa.

– Haka kuma ana bukatar mutum ya saka hoton katinsa na dan kasa ko fasfo domin tantancewa.

Idan mutum ya cike wadannan, a duk lokacin da ya bude manhajar yana da damar bukatar agajin gaggawa daga ‘yan sanda ko bayar da rahoto ko kai karar dan sanda da kuma neman agajin motar ‘yan sanda.

Bugu da kari wannan manhajar na da sashen da mutum zai iya duba ‘yan sandan da ke kusa da shi domin samun agaji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here