Kwamandojin ’yan ta’adda sun mika wuya a Borno

0
87
Borno
Borno

Wasu manyan kwamandojin Boko Haram biyu, Khaid Malam Ali da Bunu Umar sun mika wuya ga sojojin rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) a Jihar Borno.

A rahoton da kwararren mai sharhi kan harkokin tsaro da tayar da kayar baya a gabar Tafkin Chadi, Zagazola Makama ya bayar, ya ce ’yan ta’addan ISWAP sun fatattaki Ali da mayakansa bayan da suka fake a maboyar ’yan Boko Haram ta Bula Alhaji Garwaye a cikin Dajin Sambisa kusa da Karamar Hukumar Bama a ranar 5 ga Yuli, 2023.

Ali ya kasance kwamandan ’yan ta’adda a Sabil Huda da Njumia, inda ya yi ajiyar makamansa shi da wani jagoran ’yan ta’adda, Umar Buni saboda tsoron kashe su a filin yaki tare da mika kan su ga dakarun sojan na Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa ISWAP ta fatattaki Ali da mayakansa daga maboyarsu bayan da suka shirya kai farmaki kan maboyar ’yan Boko Haram a Dajin Sambisa.

Rahotanni sun ce mayakan na Boko Haram da dama ne da suka hada da matansu da ‘ya’yansu da kungiyar ta ISWAP ta kashe.

Ali kwamandan ’yan ta’adda ne a Sabil Huda da Njumia, inda ya ajiye makaman sa shi da saboda damuwar kashe shi a fagen fama.

Aminiya ta ruwaito yadda a baya bayan nan ISWAP ta kashe mayakan Boko Haram da dama, da suka hada da mata da kananan yara.

Aminiya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here