Oyo: Kotu ta daure matar da ake zargi da kashe mijinta

0
126

Wata Kotun Majistare da ke unguwar Iyaganku da ke Ibadan a jihar Oyo, ta tasa keyar wata uwa mai shayarwa mai suna Damilola Opeyemi gidan gyaran hali na Abolongo da ke garin Oyo bisa zargin kashe mijinta da wuka.

Alkalin kotun P.O Adetuyibi bai amsa rokonta ba.

Adetuyibi ya ce tsarewar na kan jiran shawarar lauyoyi daga hukumar shigar da kara ta jihar Oyo (DPP).

Don haka ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 27 ga watan Satumba.

Ana tuhumar Opeyemi da laifin kisan kai.

Tun da farko dai, dan sanda mai shigar da kara, Insifekta Olalekan Adegbite, ya shaida wa kotun cewa Opeyemi, a ranar 4 ga watan Yuli, da misalin karfe 8:30 na dare ta yi sanadin mutuwar mijinta.

Mai gabatar da kara ya ce, “Ma’auratan da ke zaune a unguwar Adogba Ajegede, Ibadan, ta daba wa mijinta, Oluwashina, mai shekaru 27 wuka, a lokacin da suke cin abincin dare.”

Ya ce laifin ya ci karo da sashe na 316 kuma ana hukunta mutum a karkashin sashe na 319 na dokokin laifuka na jihar Oyo na shekara ta 2000.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here