An kama ‘yan kasashen waje 18 da katin zabe a jihar Oyo

0
65

Hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, reshen jihar Oyo da ke kudu maso yammacin kasar ta ce ta kama ta kuma fitar da ‘yan kasashen waje 18 saboda mallakar katin zabe.

Shugaban hukumar a jihar, Isah Dansuleiman, ne ya bayyana haka a lokacin taron wayar wa da masu ruwa da tsaki kai game da zabukan da za a yi na 2023, a jiya Laraba.

Take shirin shi ne: ”Zabe mai inganci a Najeriya : Abin da ake tsammani daga baki kafin lokacin da kuma bayan zabe.”

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, wato News Agency of Nigeria, (NAN) ya ruwaito, shugaban na nbayanin cewa, sun kama bakin ne a lokacin farmakin da suka kai a sassan jihar ta Oyo.

Ya ce kasancewar bakin sun saba dokokin Najeriya a don haka aka fitar da su zuwa kasashensu.

Ya yi gargadin cewa ba wani bako komai matsayinsa a Najeriya da zai yi zaben, kuma duk wanda aka kama da katin zaben zai fuskanci hukunci.

Ya bukaci baki a jihar su zauna tare da gudabar da harkokinsu bisa doka idan har suna da takardun zama, amma kada su kuskura su shiga harkar zabe.