Daurawa ya bayyana matakan auren zawarawa a Jihar Kano

0
162
Daurawa
Daurawa

Sabon Kwamandan Hisba na Jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya shiga ofis a karo na uku, bayan sake nada shi a mukamin da gwamnan Kano Abba Kabiru Yusuf ya yi a ranar Litinin.

Sheikh Daurawa ya shugabanci Hukumar Hisba ta Kano sau biyu a jere a lokutan mulkin Rabi’u Kwankwaso da Abdullahi Ganduje.

A yayin jawabin da Babban kwamandan na Hukumar Hisba ya gabatar a harabar hukumar kafin shiga ofis don fara aiki a ranar Laraba, ya yi godiya ga Ubangiji ya kuma yi tsokaci da jan hankali da tabo tarihi da kuma neman hadin kan abokan aikinsa ‘yan Hisba da sauran ma’aikatan hukumar.

Sannan daga cikin muhimman abubuwan da Sheikh Daura ya ce zai mayar da hankali a kai a lokacin mulkin nasa, har da batun auren zawarawa.

Matakan Auren Zawarawa

Dama daya daga cikin manyan ayyukan da Hisba ta saba gudanarwa shi ne auren Zawarawa a fadin jihar.

Malam Daurawa ya bayyana cewar tuni gwamnan Kano Abba Gida-Gida ya bayar da umarnin a tantance mata da maza 2,000, wato mata dubu daya da maza dubu daya don a aurar da su bisa tallafin gwamnatin jiha.

Daurawa ya bayyana matakan da za a bi wajen tantancewa da zabo wadanda za su amfana da shirin auren kamar haka bayan kafa kwamitoci biyar
Daurawa ya bayyana matakan da za a bi wajen tantancewa da zabo wadanda za su amfana da shirin auren kamar haka bayan kafa kwamitoci biyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here