Tinubu ya nuna damuwarsa kan kashe-kashen da ake yi a jihar Filato

0
117
Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna damuwa kan tashe-tashen hankula na baya-bayan nan da ake samu a jihar Filato.

A cikin wata sanarwa da Tinubu ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan yada labarai, Dele Alake, shugaban ya yi Allah wadai da rikicin wanda ya janyo kashe-kashen rayuka a karamar hukumar Mangu da kuma wasu kashe-kashen a jihar Benuwe.

Ya ce “Ana bukatar hakuri da yafiya kan kuskuren da wani ya yi matukar ana son samar da ingantacciyar al’umma.”

Ya kara da cewa “Abin takaici ne yadda jaririya mai watanni takwas a duniya ta rasa ranta sanadiyyar rikicin da ba ta san komai ba a kai a kauyen Farin Lamba da ke jihar Filato.”

Ya bukaci shugabannin al’umma da kungiyoyin Jama’atu Nasril Islam da CAN su hada hannu domin samar da mafita ga lamarin.

Shugaban ya kuma umarci jami’an tsaro da su zakulo duk wadanda ke da hannu a kashe-kashen domin fuskantar hukunci.

Sannan ya bukaci gwamnatin jihar Filato da ta kai daukin gaugawa ga wadanda lamarin ya rutsa da su.

A farkon wannan mako ne gwamnatin jihar ta ayyana dokar hana zirga-zirga a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato bayan tashe-tashen hankula wadanda suka yi sanadin rayukan mutane da dama.

Rikicin kabilanci ya kasance ba sabon abu ba a jihar Filato.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here