Yadda sojojin Nijeriya suka murkushe ‘yan bindiga a Mangu ta jihar Filato

0
165

Rundunar sojin Nijeriya ta ce dakarunta da aka aika jihar Filato da ke tsakiyar kasar don magance rikicin da ke faruwa sun kashe wasu ‘yan bindiga.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin kasa, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya wallafa a shafin rundunar na intanet ta ce lamarin ya faru ne a karamar hukumar Mangu mai fama da rikicin kabilanci ranar Laraba.

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan hukumomin jihar sun sanya dokar hana fita ta awa ashirin da hudu a Mangu bayan barkewar rikici da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a yankin.

“Dakarun rundunar ta 3 ta sojojin kasa na Nijeriya da aka tura domin shawo kan rikicin da ke faruwa a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato sun kashe ‘yan bindiga duka a yau Laraba, 12 ga watan Yuli na 2023,” in ji sanarwar Birgediya Janar Nwachukwu.

Ya kara da cewa: “Dakarun sun kashe masu aikata laifin ne lokacin da ‘yan bindigar suka yi musu kwanton-bauna yayin da suka kai daukin gaggawa a yankin na Mangu.”

A cewar rundunar, ta share dajin da ‘yan bindigar suke samun mafaka inda ta gano bindiga uku kirar AK 47, harsasai 14 na musamman, babur guda daya da kuma katin shaida na wani karamin dan sanda.

Ta kammala da cewa yanzu haka dakarunta suna farautar ‘yan bindigar da suka tsere dauke da raunukan bindiga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here