Abun da yasa na mayar da Dala 80,000 din da na tsinta a Saudiyya – Hajiya A’ishatu Nahuce

0
135

Abin al’ajabi a kan wata mata, a she a wannan zamani akwai mutane na gari masu imani da takawa sannan kuma ga tsoron Allah a wannan duniyar sannan kuma a wannan kasar ta mu Nijeriya.

Wata Hajiya da ke aikin hajjin bana a kasa mai tsarki wato kasar Saudiyya ta tsinci Dalar Amurka 80,000 wadda a kalla idan an canza ta a Naira a kudinmu na nan gida Nijeriya kudi ne masu tarin yawa, sannan kuma ta mika su ga hukuma domin a yi cigiyar mai su, kamar yadda cibiyar kula da Alhazai ta Jihar Sakkwato ta bayyana.

Matar mai suna Hajiya Aishatu ‘Yanguru Nahuce, asali daga Zamfara take, bayan ta tsinci wannan kudin ba ta bata lokaci ba ta mika su ga hukumar Alhazai ta jihar Zamfara domin a yi cikiyar mai kudin.

An yaba wa halayyar Hajiya Aishatu, kwararren dan jarida, Sakataran watsa labarai na shugaban jam’iyar PDP na kasa, Alhaji Yusuf Dingyadi ya ce, hakika wannan baiwar Allah ba karamin jihadi ta yi ba sannan kuma ba karamar karramawa da shaidar kwarai ta samu ba ga jama’a, musamman kasancewar ta mutunniyar kirki da ke tsoron Allah da kwadayin samun rahmar Allah. Allah ya saka mata da alheri.

Maruwaita rahotannin aikin hajji ne suka sanar da hakan cikin wani sako da suka wallafa a ranar Asabar a shafinsu na Facebook.

Haka kuma, sun wallafa hoton Hajiyar wadda ta fito daga Karamar Hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara.

Muna rokon Allah ya ba ta ladan wannan gaskiya da amana da tsoran Allah da ta yi, sannan kuma Allah ya sa aikin hajjin da ta yi ya zama karbabbe Allah ya sa shi ne sanadin shigarta Aljannatul firdausi.

Tuni dai mabiya dandalin sada zumunta na Facebook suka rika bayyana ra’ayoyi mabambanta dangane da wannan baiwar Allah mai tausayi da tsoran Allah da ta yi abin a yaba mata.

A yayin da an samu masu yabawa ga wannan baiwar Allah da san kanta da ta yi daga tsoron azabar Allah ta mika wannan kudi ta san ba hakkin ta bane sannan kuma ta san idan ta ci su zai hana mata kwanciyar kabari da Hisabi shi ya sa ta mika su, a yayin da wasu kuma sun jefa ayar tambaya kan wai mai wani mahaluki zai yi da zunzurutun kudi har Dala 80,000?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here