Gasar kwallon kafar Saudi ta dara ta Amurka daraja – Ronaldo

0
168
Cristiano Ronaldo

Cristiano Ronaldo ya ce ba zai sake komawa nahiyar Turai buga tamaula ba, ya kuma kara da cewar gasar kwallon kafar Saudi Arabia ta dara ta Amurka daraja nesa ba kusa ba..

Lionel Messi ya koma taka leda a Inter Milami mai buga gasar Amurka, bayan da yarjejeniyarsa ta kare a Paris St Germain a karshen kakar 2022/23.

Ronaldo, tsohon dan wasan Real Madrid da Juventus ya koma Al Nassr cikin watan Disamba kan kwantiragin kaka biyu da rabi daga Manchester United.

Dan kwallon tawagar Portugal ya ce ya buge hanyar da fitattun ‘yan kwallo ke komawa buga gasar Saudi Arabia – yana sa ran ‘yan wasa da dama nan gaba za su koma can da taka leda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here