CCTV: Ganduje ya musanta zargin  cin bashin N10bn

0
95

Tsohon Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya musanta zargin  cin bashin N10 biliyan domin saka kyamarorin tsaro na CCTV a Birnin Kano da kewaye.

Wani gungun ƴan gwagwarmaya ƙarƙashin inuwar Coalition of Political Analysts Forum and Good Governane ya nemi gwamantin Abba Kabir Yusuf ta bincike tsohon gwamna bisa abin da ya yi da kuɗin.

Sai dai a martanin da ya fitar a Abuja, Dr Ganduje ya bai samu zarafin karɓo bashin ba saboda wata Kotun Tarayya dake Kano ta dakatar da shi bayan da Majalisar Dokoki ta amince masa.

A sanarwar da kwamishinan yaɗa labarai na gwamnatin Ganduje, Malam Muhammad Garba ya sa hannu, tsohon gwamnna ya ƙalubalanci gungun ƴan gwagwarmayar da su kawo hujjar cewa ya karɓo bashin.

Dr Ganduje ya kuma yi zargin cewa gungun ƙungiyoyin na boge ne waɗanda iyayen gidansu na siyasa ke ɗaukar nauyinsu domin ɓata masa suna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here