Ana shirye-shiryen bawa Ganduje shugaban APC na kasa

0
149

Shirye-shirye sun yi nisa na tabbatar da tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa.

Ranar Laraba da daddare ne shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gana da Ganduje da wasu gwamnoni uku kan batun.

Majiyar Aminiya ta ce Ganduje zai zama shugaban APC na riƙo zuwa lokacin da za a gudanar da babban taron jam’iyyar na bana.

Tun a ranar Litinin ne dai, bayan da shugaba Tinubu ya dawo daga taron AU a Kenya ya fara yunƙurin tabbatar da Ganduje akan wannan kujera.

Don haka ya nemi goyon bayan shugaban gwamnonin jam’iyyar APC, Hope Uzodinma na jihar Imo.

A ranar Talata Uzodinma ya gana da Ganduje kuma ya samu amincewar takwarorinsa gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC.

Ranar Laraba kuma suka gana da shugaban ƙasa tare da gwamnan Lagos Babajide Sanwo-Olu da na Ogun, Dapo Abiodun.

A nan ne aka tabbatar da zaɓin Ganduje sannan kuma suka tattauna da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima domin aiwatar da matakin.

Ministan Abuja

Kafin wannan zaɓin dai an sa ran ganin sunan Ganduje a cikin waɗanda Tinubu zai naɗa a matsayin ministoci.

Kuma an fi yi masa hasashen zama ministan Birnin Tarayya Abuja kasancewar a nan ya yi rayuwarsa ta aikin gwamnati sannna kuma digirinsa na PhD ya yi nazari ne kan yadda ake gudanar da harkokin mulki a Abuja.

Sai dai yunƙurinsa na samun minista ya samu tazgaro bayan da Hukumar yaƙi da rashawa ta jihar Kano ta fara bincikarsa game da zarge-zargen cin hanci da rashawa.

Batun da yafi jan hankali shi ne na faya-fayan bidiyon da aka nuna Ganduje na cusa Dalar Amurka a aljihu, wanda jaridar Daily Nigerian ta yi zargin cin hanci ne.

Shugaban Jam’iyya yafi Minista

Sai dai jiga-jigan jam’iyyar APC a Kano sun musanta cewa wannan binciken ne ya hana a bai wa Ganduje minista.

Wani shugaban ƙaramar hukuma da bai amince a bayyana sunansa ba ya ce ai tsohon gwamnan cigaba ya samu ba ci baya ba.

Ya ce “Mu a wurinmu wannan muƙami yafi minista domin zai ba Baba (Ganduje) damar juya jam’iyya tare da ƙarfafa alaƙarsa da shugaban ƙasa.”

Shugaban ƙaramar hukumar ya kuma musanta cewa binciken da gwamnatin NNPP ta jihar Kano ke yi wa Ganduje ne ya hana a naɗa shi ministan.

A cewarsa “wannan ba nasara ba ce ga ƴan adawa illa iyaka tsabar lissafin siyasa ne daga wurin shugaban ƙasa.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here