Jami’ar Gusau ta dauki mataki mai tsauri kan dalibai 13 marasa da’a

0
112

Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara ta dauki mataki mai tsauri na ladabtar da dalibai 13 ciki har da mata uku da aka samu da laifuka daban-daban da suka kunshi sata, coge don samun damar karatu, satar jarabawa da sauransu.

A sanarwar manema labarai da jami’in watsa labarai na jami’ar Malam Umar Usman ya fitar, ya ce, laifukan da aka samu daliban da aikatawa sun saba wa sashin doka A item (xxv) shafi na 62, da shafi 68 item (iv) na kundin tsare-tsare da dokokin da ke tafiyar da da’ar dalibai, tare da sashi L shafi 69-73 item (i-xxv) na kundin littafin dalibai.

Ya ce: “Hukumar gudanarwar jami’ar a zamanta karo na 82 da ya gudana a ranar 5 ga watan Yulin 2023 ta yi nazari da la’akari da shawarorin da rahoton kwamitin ladabtar da dalibai (SDC) ya bayar na kokar dalibai bakwai da dakatarwa/tsawaita wa’adin karatun dalibai 6 bisa samun su da laifukan rashin da’a.

“Daliban da lamarin ya shafa sun aikata laifukan da suka saba wa dokokin da ke tafiyar da harkokin dalibai na jami’ar,” ya shaida.

Ya kuma ce dauka da tabbatar da wannan matakin ya fito ne daga wajen mai rikon sakataren ilimi na jami’ar, Malam Mu’awiyya Bello a madadin rijista Malam Yakubu Audu Anivbassa da ya fitar a ranar 7 ga Yuli.

Daliban da wannan matakin na korar ya shafa sun hada da Daniel Ibeh Mayowa, Habibu Abdul, Abdulsalam Abubakar, Faruk Alayande Olamilekam, Iortim Philemon Vasue, Abubakar M. Usman tare da James Joseph.

Sannan wadanda kuma aka Dakatar da karatunsu na wasu lokuta daga zangon karatu daya wasu zangon karatu biyu; Emmanuel Chibuzor Ejikeme, Idowu Ojo Oni, Khadija Abdulrahman Bala, Sadiya Sani Garba, Balkisu Bello da kuma Ibrahim Mu’azu Lawal.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here