Shugabannin jam’iyyar NNPP 9 sun fice daga jam’iyyar

0
150
NNPP

Shugabanin jam’iyyar NNPP na kananan hukumomi guda tara a jihar Katsina sun aje muƙamansu sun kuma fice daga jam’iyyar.

Sanarwar na ƙunshe acikin wasika da shuwagabannin suka sanya ma hannu tare da tura ta ga shugaban shugaban jam’iyyar NNPP na jihar katsina.

Sai dai basu bayyana dalilin ɗaukar wannan matakin ba sai dai sun ɗauki matakin bisa wani dalili na sirri kamar yadda suka bayyana.

Daga ƙarshe sunyi godiya ga shugabannin jam’iyyar bisa damar da aka basu na zama shugabannin jam’iyyar a kananan hukumomin da suka fito.

Katsina Post ta ruwaito cewa Shugabannin kananan hukumomin sun haɗa da na:

1.Katsina Local Govt

2.Batagarawa LG

3.Rimi LG

4.Jibia LG

5.Batsari LG

6.kaita LG

7.Safana LG

8.Dutsima LG

9.Charanci LG.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here