Shari’ar zaben Kano: Rashin bayyanar shaidun Abba Gida-Gida a kotu yasa hana shi fara kariya

0
91
Gawuna & Abba Gida Gida

Rashin halartar shaidu uku na Abba Kabir-Yusuf na jam’iyyar NNPP ranar juma’ar nan, ya hana shi fara yin kariya a Shari’ar zaɓen gwamnan kano da jam’iyyar APC ta shigar a gaban kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Kano.

NAN ta ruwaito cewa masu shigar da kara jam’iyyar APC na kalubalantar INEC kan ayyana Abba Kabir-Yusuf na NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023.

Wadanda APCn take kara sun hada da INEC, Abba Kabir-Yusuf da kuma jam’iyyar NNPP .

A lokacin da aka kira karar, Lauyan Abba Kabir-Yusuf, Mista Eyitayo Fatigun SAN, ya shaida wa kotun cewa shaidu ukun da suke son gabatar wa ba su sami damar halartar zaman Kotun ba.

“Muna ba da hakuri saboda shaidun uku sun sami matsalar jirgin a kan hanyarsu ta zuwa Kano daga Abuja. Ya mai Shari’a muna neman a dage shari’a” inji Fatigun

Lauyan INEC, Emmanuel Osayomi da Lauyan NNPP, John Olusola SAN, ba su yi adawa da bukatar hakan ba.

Shi ma lauyan wanda ya shigar da kara, Offiong Offiong SAN, bai yi adawa da bukatar dage shari’ar da wanda ake kara na biyu ya nema ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here