An Ƙaddamar da sabuwar rundunar ‘Hakorin Damusa’ da za ta yaki fadan kabilanci a Filato

0
139

Babban hafsan sojin ƙasa na Nijeriya Manjo Janar Taoreed Lagbaja ya ƙaddamar da sabuwar rundunar soji mai suna ‘Haƙorin Damisa’ da za ta yi yaƙi da rikicin ƙabilanci da na tsakanin manoma da makiyaya a ƙaramar hukumar Mangu da ke jihar Filato.

BBC ta rawaito wani sakon Twitter da rundunar sojin ƙasan Nijeriya ta wallafa, ta ce an ƙaddamar da rundunar ne domin magance tashe-tashen hankulan da ake yawan samu, a ƙaramar hukumar, lamarin da ke ƙara haifar da taɓarɓarewar tsaro a yankin.

Yayin da yake jawabi ga dakarun rundunar, a lokacin ƙaddamarwar, babban hafsan soji ƙasa na Nijeriyar ya yi kira a gare su da sun kawar da duka wani nau’in barazanar tsaro da yankin ke fuskanta da ma jihar Plateau baki-ɗaya.

Manjo Janar Lagbaja ya ce dakarun su tabbatar sun yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da tsaron lafiyar mazauna yankin, ta hanyar gaggauta kai ɗauki a duk inda aka buƙace su.

Ya kuma sake nanata wa sojojin irin ƙwarin gwiwar da al’umma gari ke da shi a kansu.

Haka kuma babban hafsan sojin ƙasar ya gana da masu ruwa-da-tsaki na ƙaramar hukumar, inda ya yi kira a gare su, da su nuna kishi wajen maido da zaman lafiya a ƙaramar hukumar, wani abu da ya kira ”Babban aikin maido da zaman lafiya a Mangu”.

Yana mai cewa babu wanda zai kai al’ummar garin tare da iyalansu jin daɗi, idan aka samu samu zaman lafiya a yankin.

A baya-bayan nan dai an samu rahotonnin tashe-tashen hankula a garin na Mangu.

Jihar Plateau na daga cikin jihohin Nijeriya da ke yawan fama da rikice-rikice masu alaƙa da addini da ƙabilanci da na manoma da makiyaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here