Elon Musk ya sauya tambarin Twitter

0
147

Shugaban Twitter Elon Musk da babbar jami’ar kamfanin Linda Yaccarino sun kaddamar da sabon tambarin shafin na sada zumunta mai taken “X” .

Hakan na nufin daga yanzu an daina amfani da alamar tsuntsu a matsayin tambarin Twitter.

“Muna gabatar muku da X!,” in ji wani sakon Twitter da Yaccarino, inda kuma ta wallafa hoton da ke nuna tambarin a jikin ginin ofishin Twitter da ke birnin San Francisco ranar Juma’a.

Yanzu dai shafukan Twitter na jama’a da ke amfani da shafin sun sauya daga tsuntsuwa zuwa alamar X.

Ranar Lahadi ne Musk ya bayyana cewa yana so ya sauya tambarin na Twitter.

Ya wallafa hoton tambarin X a shafinsa.

Musk ya kawo sauye-sauye da dama a kamfanin ciki har da takaita adadin bayanan mutanen da masu amfani da shafin za su iya gani.

Wadannan sauye-sauye sun jawo muhawara sosai a fadin duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here