Magidanci ya hallaka saurayin matarsa a Adamawa

0
118

An gurfanar da wani magidanci a kotu bisa zargin ya kashe wani matashi da yake zargi yana neman matarsa a jihar Adamawa.

Ana zargin magidancin da hada kai da kaninsa wajen lakada wa mamacin duka har lahira ne bayan da ya kama su tare da amaryar tasa.

Dan sanda mai gabatar da kara, Sufeto Zakka Musa ya shaida wa kotu cewa magidancin da dan uwan nasa sun far wa mamacin ne da adduna da sanduna, suka yi ajalinsa; an garzaya da shi asibitin da ke garin Fufore, amma likitoci suka ce ya riga ya rasu.

Amma da yake ba da bahasi, magidancin mai shekaru 20 ya shaida wa kotu cewa ya sha jan kunnen mamacin cewa ya daina neman matarsa, amma ya ki ji.

Ya ce fada ne ya kaure a tsakaninsu, bayan sun bi sawun mamacin suka kama shi tare da amaryar tasa da aka daura musu aure bara.

A cewarsa, mamacin ne ya fara bugun sa da sanda, shi ne kaninsa ya kawo masa dauki, suka ga bayansa, amma ya musanta cewa sun yi amfani da adda a lokacin fadan.

Bayan sun amsa zargin ne Babbar Kotun Majistare da ke Yola ta sa a tsare su zuwa ranar 27 ga watan nan na Yuli.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here