Rikicin Mangu: Sama da mutum 80,000 sun rasa muhallansu cikin wata uku

0
110

Akalla mutum 80,000 sun tsere daga gidajensu cikin wata uku sakamakon rikicin kabilancin da ke faruwa a Mangu jihar Filato, a cewar wani babban jami’in gwamnati, a yayin da aka tura karin sojoji domin shawo kan matsalar.

Tun watan Mayu an samu karuwar barkewar rikici tsakanin manoma da makiyaya musamman a Mangu lamarin da ya kai ga mutuwar kusan mutum 300, a cewar shugaban karamar hukumar.

Hakan ne ya sa Babban Hafsan Sojin Kasa na Nijeriya Manjo Janar Taoreed Lagbaja ya kai ziyara Mangu a karshen makon jiya, kuma ya sha alwashin “kawar da rikicin gaba dayansa.”

Rundunar tsaro ta Operation Safe Haven ta kai hedikwatarta Mangu, sannan ta tura karin sojoji 300 da kayan aiki domin shawo kan matsalar.

“Ku yi aiki tare da mutanen gari. Ku sojojin al’umma ne don haka dole ku kai musu dauki cikin gaggawa idan suka nemi hakan daga gare ku,” a cewar Manjo Janar Taoreed Lagbaja.

Kiyasi ya nuna cewa rikicin ya raba mutum 80,000 daga gidajensu kuma yanzu suna zaune a sansanoni 11 da ke karamar hukumar nan,” a cewa shugaban karamar hukumar Mangu Markus Artu, a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na AFP.

Ya kara da cewa mutum 18,000 daga cikin wadanda rikicin ya kora daga muhallansu na samun mafaka a wata makarantar firamare.

Daya daga cikin masu kula da sansanonin Yamput Daniel ya tabbatar wa AFP da wannan adadi.

“Rikicin ya raba mu da gidajenmu, an lalata gonakinmu kuma an bar mu da samun mafaka a makarantar firamare,” a cewar Grace Emmanuel, mai shekara 70.

Hukumomin bayar da agaji suna ci gaba da kai wa mutanen tallafi, sai dai kawo yanzu ba su fitar da rahoto game da adadin mutanen da rikicin ya raba da gidajensu ba.

Kungiyoyin makiyaya da ke yankin sun ce rikicin ya raba su da muhallansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here