Kungiyar Kwadago ta baiwa Tinubu kwana 7 ya dawo da tallafin man fetur ko ta shiga yajin aiki

0
183

Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC) ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki bakwai da ta janye karin farashin man fetur na baya-bayan nan ko kuma ta fuskanci yajin aikin da ba za ta taba mantawa da shi ba a fadin kasar nan daga ranar 2 ga watan Agustan 2023.

“Saboda haka, NLC ta umarci ‘ya’yanta da ke jihohi da su gaggauta fara tattara ma’aikata da sauran ‘yan Nijeriya, ciki har da sauran kungiyoyin farar hula, don gudanar da yajin aikin da zai dauki tsawon lokaci ana gudanar da zanga-zanga, idan har gwamnati ta gaza biyan bukatunta.”

An tattaro cewa wannan na daya daga cikin shawarwarin da aka cimma a taron kwamitin tsakiya NLC da CWC, wanda aka gudanar a ranar Talata, 25 ga watan Yuli, a Abuja.

Janye tallafin man fetur da shugaba Tinubu ya yi ya jefa talakawan Nijeriya cikin matsin rayuwa.

Lamarin da ya sanya kowa yin kuka game da halin matsin tattalin arziki da ake fuska.

Tun da fari NLC ta so shiga yajin aiki amma wata kotun tarayya ta dakatar da ita a watan Yunin da ya gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here