Bayern Munich na kokarin ɗaukar Kane

0
43

Bayern Munich na fatan daukar Harry Kane daga Tottenham duk da cewa PSG na neman dan wasan.

Su kuwa shugaban Bayern Munich din Jan-Christian Dreesen da kuma daraktanta Marco Neppe ba su bi ƙungiyar Japan ba, a maimakon haka sun tsaya don hada kudin da za su sayi Kane din fam miliyan 100.

PSG na sa ran samun kudi hadi da dan wasa daga kungiyoyin Turai da ke son daukar Kylian Mbabbe wanda Al-Hilal ta taya a kan kudi fam miliyan 259, yayin da su ma kungiyoyin kamar Chelsea da Manchester United da Tottenham da Inter Milan da kuma Barcelona ke sha’awar dan gaban Faransa mai shekara 24.

Manchester City ta shaida wa dan tsakiyar Portugal Bernardo Silva cewa ba su da niyyar sayar da shi a kakar bana duk da sha’awar da dan wasan mai shekara 28 ke da ita ta matsawa daga kungiyar.

West Ham ta tattauna da Manchester United a kan daukar dan bayan Ingila Harry Maguire,mai shekara 30 da kuma dan tsakiyar Scotland Scott McTominay, mai shekara 26.

To amma West Ham din ta jinkirta tayin da ta yi wa Mc Tominay na fam miliyan 40.

Haka zalika Hammers din ta taya dan tsakiyar Chelsea Conor Gallagher, mai shekara 23, amma Chelsea ta yi watsi da tayin, ko da yake Hammers din na sa ran za a sayar mata da dan wasan maimakon Tottenham.

Ita kuwa Southamton watsi ta yi da tayin fam miliyan 35 daga Liverpool a kan dan tsakiyar Belgium Romeo Lavia, inda ta ke son a bata fam miliyan 50.

Cinikin dan tsakiyar Liverpool dan kasar Brazil Fabinho da Al-Ittihad na cikin kila wakala, don haka dan wasan mai shekaru 29, ke shirye-shiryen komawa wasannin share fage da kungiyar ta Liverpool.

Dan tsakiyar Jamus Joshua Kimmich na duba yiwuwar tsayawa a Bayern Munich bayan da dan wasan ya ce yana da tabbacin zai buga kungiyar wasannin Bundesliga a kaka mai zuwa.

Everton na tattaunawa a kan dawo da dan gaban Italiya Wilfried Gnonto, mai shekaru 19 daga Leeds United.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here