Likitocin Nijeriya sun shiga yajin aiki

0
148

Kungiyar likotoci masu neman kwarewa ta kasa ta Nijeriya ta soma yajin aiki na sai baba ta gani ranar Laraba.

Wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce ta tsunduma yakin aiki ne don neman gwamnati ta kara wa mambobinta albashi da alawus-alawus.

Kazalika kungiyar ta yi korafi game da yadda aka tsame wasu daga cikin mambobinta daga kudin ariyas da ake bayarwa tana mai yin kira ga gwamnati ta biya su kudin.

Kungiyar likitoci ta Nijeriya ta ce a kowanne mako likitoci hamsin na balaguro su fice su bar kasar sakamakon haka.

Yajin aikin likitoci na matukar shafar harkokin kiwon lafiya musamman a asibitocin gwamnati da ke lardin kasar.

A ranar Litinin ne shugaban majalisar wakilan Nijeriya Tajudeen Abbas ya yi kokarin rarrashin kungiyar likotocin don kada ta shiga yajin aikin amma ta ki yarda kwata-kwata da muradinsa.

Ranar 5 ga watan nan na Yuli ne kungiyar likitocin ta ja kunnen gwamnatin kasar ta hanyar bata wa’adin mako biyu don ta biya mata bukatunta idan ba haka ba ta shiga yajin aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here