Tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya sanyawa shugaban kasa Bola Tinubu jerin sunayen ministocin da aka karanta a zauren majalisar dattawa da yammacin ranar Alhamis.
Tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi; tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El Rufa’i; da mai magana da yawun shugaban kasa, Dele Alake shi ma ya sanya jerin sunayen.
Bayan dogon jiran da ‘yan Najeriya suka yi, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, a ranar Alhamis, ya gabatar da jerin sunayen ministocin Tinubu a gaban majalisar dattawa.
Gbajabiamila, wanda shi ne tsohon kakakin majalisar wakilai, ya gabatar da jerin sunayen ga shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da misalin karfe 01:19 na rana.
Daga nan ne Akpabio ya karanta jerin sunayen ministoci tare da sunayen mutane 28.
Jerin sunayen ministocin;
Abubakar Momoh
Yusuf Maitama Tukur
Ahmad Dangiwa
Hannatu Musawa
Uche Nnaji
Betta Edu
Diris Anite Uzoka
Dauda Umahi
Ezenwo Nyesom Wike
Abubakar Badaru
Nasiru El Rufa’i
Ekerikpe Ekpo
Nkiru Onyejiocha
Olubunmi –
Stella Okotete
Uju Kennedy Ohaneye
Bello Muhammad Goronyo
Dele Alake
Lateef Fagbemi
Mohammed Idris
Olawale Edun
Waheed Adebanwo
Sulaiman Ibrahim
Ali Pate
Joseph Usev
Abubakar Kyari
John Enoh
Sani Abubakar Danladi