Juyin Mulki: Alhazan Najeriya 360 sun makale a Nijar

0
99

Wani jirgi mallakin kamfanin jiragen sama na Max Air ya makale a filin sauka da tashin jiragen sama na Diori Hamani da ke Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar bayan juyin mulkin da aka yi a kasar.

Rahotanni sun ce jirgin, mai lamba 5N-ADM, ya sauka a Yamai ne bayan ya kwaso alhazan kasar daga kasar Saudiyya.

Sai dai ba zai iya tashi ya bar birnin ba saboda rashin tabbas din da aka shiga, sakamakon hambarar da Shugaban Kasar, Mohammed Bazoum, da sojojin kasar suka yi a ranar Laraba.

Jirgin, a cewar rahotanni, ya sauka a Yamai ne da alhazan Najeriya su 360 wajen misalin karfe 10:40 na daren Laraba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here