Jerin sunayen ministoci: El-Rufa’i, Wike, Alake da Oyetola da sauransu

0
110

Shugaba Bola Tinubu ya aike da sunayen tsoffin gwamnonin Ribas, da Kaduna da Osun da kuma Kross Riba a matsayin ministoci. Wadanda aka nada su ne: Nyesom Wike, Nasir E-Rufai, Gboyega Oyetola, da Ben Ayade.

Sauran da ke cikin jerin sunayen ministocin da za a bayyana a zauren majalisar dattawan a safiyar yau Alhamis sun hada da babban hadimin shugaba Tinubu, Dele Alake; Lateef Fagbemi; Shugabar mata ta APC ta kasa, Dokta Betty Edu; tsohon kwamishinan kudi na Jihar Legas, Wale Edun; Tsohon Ministan Lafiya, Farfesa Ali Pate, da kuma tsohon mataimakin gwamnan CBN, Adebayo Adelabu, daga jihar Oyo.

An ruwaito cewa Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ya bayyana a kwanaki biyu da suka wuce, cewa Shugaban kasa ya ce da kansa zai shirya jerin sunayen ministoci zuwa ranar Alhamis, don haka yana bukatar addu’ar ‘yan Nijeriya don ya zama ya nada mutanen da suka dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here