Sojoji sun yi wa shugaban kasar Nijar juyin mulki

0
65

Sojojin sun bayar da sanarwa ne ta gidan talbijin na kasar cewa sun tsige shugaban kasar, Mohamed Bazoum, daga mukaminsa tare da rufe dukkan iyakokin kasar.

Sanarwar ta ce an rufe dukkan hukumomi da ma’aikatu a Nijar tare da sanya dokar hana fita.

Yanzu haka dai babu wani labari da yake tabbatar da halin da shugaba Mohamed Bazoum ke ciki a yanzu.

Kakakin sojojin ƙasar Manjo Ahmadou Abdourahamane ne ya sanar da juyin mulkin.

Sun sanar da rushe kundin tsarin mulkin ƙasar da rufe dukan iyakokin ƙasar baki ɗaya.

sojojin sun ce sun yi juyin mulkin ne saboda halin da Nijar ke ciki na taɓarɓarewar tsaro da tattalin arziƙi.

Wani rahoton BBC ya ce, Shugaban ƙasar Benin Patrice Talon wanda ke jagorantar tawagar ECOWAS na cikin ƙasar, sai dai sun gaza cimma wata yarjejeniya da masu gadin shugaban ƙasar da suka amshe mulkin.

Tun a safiyar jiya Laraba ne aka bayar da rahotannin tsare Shugaba Bazoum a gidan gwamnati, abin da ya janyo zanga-zanga daga magoya bayan Bazoum.

Sojoji sun yi harbe-harben jan kunne domin tarwatsa masu zanga-zangar.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya nuna rashin goyon bayan wannan ƙasarsa kan juyin mulkin.

Sakataren Majalisar ÆŠinkin Duniya Antonio Guterres ya ce ya yi magana da Shugaba Bazoum kuma ya tabbatar masa da cewa yana da goyon bayan Majalisar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here