Gwamnatin Kano ta soke lasisin Kannywood

0
93

Gwamnatin jihar Kano ta soke lasisin masana’antar Kannywood da gidajen Gala.

Shugaban hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta jihar Kano, Malam Abba El-Mustapha ne ya sanar da haka da safiyar Juma’a.

El-Mustapha ya ce hakan na nufin babu wanda zai ci gaba da yin fim a jihar Kano sai ya sabunta rajista da hukumar.

Wannan soke lasisin ya shafi masu fitowa a fim, da masu shiryawa, da kasuwancinsa.

Su kuma gidajen rawar Gala an dakatar da su nan take har sai an tantance su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here