Juyin mulki: Mun lashi takobin tabbatar da dimokuradiyya a Nijar – ECOWAS

0
117

Shugaban Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) kuma Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya mayar da martani kan rikicin siyasa a Jamhuriyar Nijar, inda ya bayyana goyon bayan kungiyar ga zababbiyar gwamnatin dimokuradiyya a kasar.

Tinubu ya jaddada cewa ECOWAS ta lashi takobin tabbatar da mulkin dimokuradiyya da tsarin mulki a kasar ya shimfida tare da gargadin sojojin da ke kwadayin mulki ko ta halin kaka su shiga taitayinsu.

Tinubu ya jaddada cewa yankin zai tsaya tsayin daka wajen goyon bayan zababbiyar gwamnati a Nijar. Ya jaddada muhimmancin kiyaye dimokuradiyya ga al’ummar Nijar da zaman lafiya da ci gaban yankin yammacin Afirka baki daya.

Ya ce, “Bayanan da ke fitowa daga Jamhuriyar Nijar na nuni da cewa wasu abubuwa marasa dadi na faruwa a kan manyan shugabannin siyasar kasar.

“Ya kamata duk wadanda suke da hannu a lamarin sun san cewa shugabannin yankin ECOWAS da duk masu kaunar dimokuradiyya a duniya ba su goyi bayan wannan lamari ba.
“Shugabannin ECOWAS ba za su amince da duk wani mataki da zai kawo cikas ga halattacciyar gwamnatin Nijar ko wani yanki na yammacin Afirka ba.

“Ina so sanar da cewa muna sa ido sosai kan al’amura da abubuwan da ke faruwa a Nijar kuma za mu yi duk abin da ya dace don tabbatar da cewa dimokuradiyya ta kafu, ta bunkasa, da tushe mai kyau a yankinmu.
“Ina tuntubar sauran shugabannin yankinmu, kuma za mu kare dimokuradiyyar da muke buri bisa ka’idar tsarin mulki wanda kowa ya yarda da shi.

“A matsayina na shugaban kungiyar ECOWAS, ina jadadda aniyar goyon bayan Nijeriya ga zababbiyar gwamnati a Nijar, sannan ina tabbatar da cewar shugabannin ECOWAS ba za su bar Nijar cikin jimami ba, sai mun tsaya tsayin daka don kiyaye tsarin mulkin kasar.”

Kungiyar kasashen yankin ta kara da cewa ba za ta lamunci sake juyin mulki a yammacin Afirka ba.
Nijar kasa ce da ba ta da ruwa a yammacin Afirka, wadda ta fuskanci juyin mulki hudu tun bayan samun ‘yancin kai daga Faransa a 1960, da kuma yunkurin juyin mulki da dama.

Shugaba Bazoum, wanda aka zaba ta hanyar dimokuradiyya a shekarar 2021, ya kasance babban abokin kasar Faransa da ta yi wa kasar mulkin mallaka.

Juyin mulki na karshe a kasar ya faru ne a watan Fabrairun 2010, wanda ya hambarar da shugaba Mamadou Tandja na lokacin.

Nijar dai na fama da boren mayakan Jihadi guda biyu – daya a kudu maso yammacin kasar, wanda tagayyara makwabciyar kasar Mali a shekarar 2015, dayan kuma a kudu maso gabas, wanda ya hada da mayakan jihadi dake arewa maso gabashin Nijeriya.

Kungiyoyin masu fafutuka da ke da alaka da al-Kaeda da kuma kungiyar IS sun addabi kasar a shekarun baya-bayan nan wanda ya kai ga mutuwar mutane.

Kasashen Yammacin Afirka na kara fuskantar matsalar juyin mulki a ‘yan kwanakin nan. Mali Guinea da Burkina Faso sun fuskanci juyin mulki kwanan nan a cikin mawuyacin hali na tattalin arziki da talauci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here