MDD ta dakatar da ayyukan jinkai a Nijar bayan juyin mulki

0
84

Ofishin Ayyukan Jinkai na Majalisar Dinkin Duniya, OCHA, ya dakatar da dukkan ayyukansa a Jamhuriyar Nijar bayan juyin mulkin da sojojin kasar suka yi.

A wata sanarwa da ofishin na OCHA ya fitar da maraicen ranar Alhamis, ya ce “Sakamakon abubuwan da ke faruwa a Nijar, mun dakatar da ayyukan jinkai da muke yi a can, inda da ma kasar ke fuskantar yanayin jinkai mai sarkakiya da ke da alaka da karuwar tashin hankali da kalubalen zamantakewa da kuma sauyin yanayi.”

Fadar shugaban kasar Nijar ta tabbatar da cewa sojojin kasar wadanda suka toshe hanyoyin shiga fadar tun a ranar Laraba sun hambarar da Shugaba Muhamed Bazoum.

A yayin da yake ayyana goyon bayansa ga dakarun da suka kaddamar da juyin mulkin, shugaban rundunar sojin kasar ya ce matakin ya zama dole ne don “a hana mummunan fito-na -ito tsakanin rundunoni daban-daban.”

Miliyoyin mutane na bukatar abinci

Yawan mutanen da ke bukatar agaji ya karu daga miliyan 1.9 a 2017 zuwa miliyan 4,3 a 2023 a Nijar, a cewar ofishin OCHA.

Fiye da mutum 370,000 ne suka rabu da muhallansu da suka warwatsu a cikin kasar don neman mafaka, baya ga ‘yan gudun hijira 250,000 da da ma suke neman mafaka a kasar – wadanda suka je daga kasashe irin su Nijeriya da Mali da kuma Burkina Faso.

Kazalika ana sa ran yawan masu tsananin bukatar abinci zai karu daga miliyan 2.5 zuwa miliyan uku a lokacin damina, daga tsakanin watan Yuni zuwa Agusta, a cewar hukumar ta MDD.

A yanzu haka MDD ta ware dala miliyan 584 don aiwatar da ayyukan agaji a kasar.

‘Ba a kammala juyin mulki ba’

A gefe guda, Ministar Harkokin Wajen Faransa Catherine Colonna ta bayyana cewa masu yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar “ba su kammala shi ba”.

Ta bayyana haka ne ranar Juma’a inda ta ce shugaban Faransa Emmanuel Macron ya tattauna da Shugaba Mohamed Bazoum kuma yana cikin koshin lafiya.

Colonna ta ce tana fata masu juyin mulkin za su saurari kiran da duniya ke yi musu na su janye daga wannan ta’ada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here