Juyin mulki: Amurka za ta bai wa Mohamed Bazoum taimako ‘mara iyaka’

0
74

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya ce kasarsa za ta bai wa shugaban kasar Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum taimako “mara iyaka” sannan ya “jaddada muhimmancin ci gaba da mulkinsa” a kasar.

Mr Blinken ya bayyana haka ne a tattaunawar da ya yi ta wayar tarho da Mohamed Bazoum, a cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar ranar Juma’a.

“Ya jinjina wa Bazoum a kan rawar da ya taka wajen tabbatar da tsaro a Nijar da kuma yankin Yammacin Afirka,” in ji sanarwar da kakakin ma’aikatar wajen Amurka Matthew Miller ya fitar.

Sanarwar na zuwa ne awanni bayan Janar Abdourahamane Tchiani da ya jagoranci juyin mulki a kasar ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban kasa sannan ya yi gargadin cewa za a zubar da jini idan wata kasar waje ta tsoma baki a sha’anin cikin gida na Nijar.

Sanarwar ta kara da cewa “Sakatare Blinken ya jaddada cewa Amurka za ta ci gaba da aiki tukuru wajen ganin an dawo da tsarin mulki da na dimokuradiyya a Jamhuriyar Nijar.”

Kazalika Mr Blinken ya yi magana ta wayar taro da tsohon shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou, inda ya bayyana masa “matukar damuwar ganin ana ci gaba da tsare Bazoum, shugaban da aka zaba a turbar dimokuradiyya.”

Ya kara da cewa ya damu da yadda aka kasa shawo kan matsalar da ta faru don dawo da tsarin mulki da doka a kasar.

“Sakatare yana takaici game da yadda mutanen da suka tsare Bazoum ke barazana ga nasarar da aka samu ta hada kai da kuma taimakon miliyoyin dalolin da ake bai wa al’ummar Nijar,” in ji sanarwar.

Blinken ya bukaci Issoufou ya “cigaba da kokarin ganin an magance matsalar don samun nasarar gwamnatin dimokuradiyyar da aka zaba,” a cewar Miller.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here