Tinubu ya nada wanda zai binciki CBN da sauran hukumomin da ke tare da bankin

0
164

Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin binciken babban bankin Nijeriya (CBN) da hukumomi da bangarorin da ke tare da bankin.

Tinubu Ya nada nada wani mai bincike na musamman, Jim Osayande, domin gudanar da wannan aiki.

Umurnin na kunshe ne a cikin wata takarda mai taken ‘Sirri’ wacce shugaba Tinubu ya sanya wa hannu da kansa, LEADERSHIP ta gani a ranar Lahadi.

“A kan kudurin da aka bayyana a sashe na 15 (5) na kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima), gwamnati a yau ta ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa ta hanyar nada ka (Jim Osayande) a matsayin mai bincike na musamman, domin gudanar da binciken CBN da hukumomi da bangarori da ke da alaka da CBN. Wannan nadin ya fara aiki nan take kuma za ku dinga kawo rahoto kai tsaye zuwa ofishi na.” Wani bangare na takardar mai taken ‘Sirri’

Wannan umurnin na zuwa ne a dai dai lokacin da tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya CBN, Godwin Emefiele, ke fuskantar shari’a kan zargin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba a gaban babbar kotun tarayya da ke Legas.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here