An yi zanga-zanga kan tsadar rayuwa a Kano

0
113
Zanga Zanga
Matasa

Gamayyar wasu ƙungiyoyi sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin daɗi kan abin da suka kira matsi da ƙuncin rayuwar da ‘yan kasar suka tsinci kansu a ciki.

‘Yan ƙungiyoyin waɗanda suka bazu kan wasu titunan Kano, sun haɗar da ƙungiyar dalibai, inda suke neman gwamnati ta sassauta yanayin da ake ciki na tsadar rayuwa.

Masu zanga-zangar maza da mata, wasunsu ɗauke da allunan rubuce-rubuce, sun yi korafi a kan wahalhalun da suka ce janye tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi, ya jefa mutane cikin mawuyacin hali.

Ƙungiyoyin sun hada da na mata da ɗalibai da kuma masu rajin kare haƙƙin ɗan’adam.

Ɗaya daga cikin masu zanga-zangar, Kwamared Fatima Muhammad Umar ta ce babban abin da ya fi tayar mata da hankali shi ne mata ne suka fi shiga tasku sanadin wahalhalun da ake fama da su a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here