Denmark za ta yi dokar haramta kona Al-Qur’ani

0
98
Al-Qur’ani
Qur'an

Gwamnatin Denmark ta mika wa Majalisar Dokokin Kasar bukatar amincewa da kudirin haramta kona Al-Qur’ani mai girma da sauran litattafan addini a gaban Ofishin Jakadancin kasashe.

Ministan Harkokin Wajen Kasar, Lars Lokke Rasmussen ne bayyana hakan ta cikin wata tattaunawa da kafar talabijin din kasar wato DR.

Ya bayyana cewa lokaci ya yi da kasar za ta haramta kona litattafan addini da nufin tunzura mabiya addinin.

Ministan, wanda ke bada misali da abin da ya faru a baya-bayan nan, ya ce kona Al-Qur’anin da aka rika yi a kasar kawai don ya faru a kasar Sweden ya janyo mata asara da kuma zubewar kima da lalata alakar diflomsaiyya tsakaninta da manyan kasashen Musulmi da ta ke hulda da su.

Ya kuma bayyana cewa Firaministan kasar, Matte Frederisken tuni ya mika bukatar samar da wannan doka, abin da ya rage yanzu kawai shi ne sahalewar ‘yan majalisa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here