Abdulsalami ya jagoranci tawagar ECOWAS zuwa Nijar domin yin sulhu da sojoji

0
155
Abdulsalami Abubakar

Shugaban ƙungiyar Ecowas, Bola Ahmed Tinubu, ya tura wata tawaga zuwa jamhuriyar Nijar domin yin sulhu da sojojin da suka yi juyin mulki.

Hakan na cikin matakan da Ecowas ta cimma a taron gaggawar da ta yi a cikin hutun ƙarshen makon da ya gabata a Abuja.

Tsohon shugaban mulki soji na Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar ne ke jagorantar tawagar.

Sauran yan tawagar sun haɗa da Sarkin Musulumi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III da kuma shugaban hukumar ƙungiyar Ecowas Omar Alieu Touray.

Shugaban na Ecowas ya kuma tura wata tawagar ta daban ƙarƙashin jagorancin Ambasada Babagana Kingibe, zuwa Libya da Aljeriya kan batun juyin mulkin Nijar ɗin.

Shugaba Tinubu ya nemi da su zauna da duk masu ruwa da tsaki tare da yin bakin ƙoƙarin su wajen samar da mafita kan halin da ake ciki a Nijar.

Shugabannin tawagogin biyu sun bayyana cewa za su yi bakin ƙoƙarinsu domin tabbatar da samun abin da su ka je nema.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here