Zamu tabbatar da nasarar APC a zaben gwamnan jihar Kogi, Imo da Bayelsa – Ganduje

0
84
Ganduje

Sabon shugaban jami’iyar APC mai mulki, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce zai kama aiki ba ji ba gani domin tabbatar da jam’iyyarsa ta yi nasara a zaÉ“en gwamnan jihohin Kogi da Bayelsa da za a gudanar ranar 11 ga watan Nuwamban 2023.

Ganduje ya bayyana haka ne a yau Alhamis, lokacin da yake jawabi bayan tabbatar da shi a matsayin shugaban jam’iyyar APC, a wajen taron majalisar zartarwar jam’iyyar da ya gudana a Abuja.

An kuma zaÉ“i tsohon mai magana da yawun Majalisar Dattijan Najeriya, Ajibola Basiru, É—an jihar Osun a matsayin sakataren Jam’iyar.

A jawabin nasa, Ganduje ya gode wa Shugaba Bola Tinubu, ya kuma jaddada cewa zai tabbatar da zaman lafiyar a cikin jam’iyar.

Ganduje ya yi alÆ™awarin yin aiki tuÆ™uru wajen tabbatar da nasarar jam’iyar a zaÉ“en gwamnan jihar Kogi da Imo da Bayelsa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here