Sojoji sun katse wutar lantarki a ginin da suke tsare da Bazoum

0
138

Jam’iyyar PNDS Tarayya ce ta sanar da wannan matakin da sojojin suka dauka yayin da a daya gefen kuma hukumomin sojin ba su ce uffan ba kan lamarin.

Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun katse wutar lantarki a bangaren ginin da hambararen shugaban kasa Mohamed Bazoum ke ajiye. 

Tun a yammacin Talata ne aka fara fuskantar matsalar wutar lantarki a Nijar bayan da Najeriya ta katse layin wutar da ta ke bai wa kasar a wani bangare na takunkumin da kungiyar ECOWAS ta kakaba wa kasar da nufin tilasta wa sojoji su maida Bazoum kan mukaminsa.

A sanarwar da ta bayar kan wannan batu, jam’iyar PNDS Tarayya ta ce hukumomin mulkin sojan sun cire layin da ke ba da wuta a ginin da shugaba Mohamed Bazoum ke tsare tun da misalin karfe 11 na ranar Laraba 2 ga watan Agusta.

Wasu na kallon matakin a matsayin huce takaici. Kawo yanzu sojojin ba su musanta wannan zargi ba.

A dai gefe gidan rediyon Faransa na RFI da tashar talbijan ta France 24 sun dakatar da shirye-shiryensu a kasar ta Nijar.

Sai dai kawo yanzu hukumomin gidan Rediyon na RFI sun ce ba su da masaniya idan hukumomin kasar ne suka rufe tashar ko akasin haka domin ba su sami wata takardar da ke sanar da su daukan irin wannan mataki ba.

VOA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here