NNPP na barazanar korar Kwankwaso

0
313

Kungiyar shugabannin jam’iyyar New Nigeria People’s Part (NNPP) ta bukaci dan takararta na shugaban kasa a zaben da ya gabata, Sen. Rabiu Kwankwaso da ya mika mata takardar murabus nan take ko kuma a dakatar da shi ba tare da wani lokaci ba, saboda zarginsa da hannu a cikin harkallar jam’iyyar.

Wanna na zuwa ne a sakamakon zargin Kwankwaso da yin amfani da rigar jam’iyyar wajen cimma manufarsa ta siyasa, musamman kyautata alaka da APC mai mulki.

Shugabannin jam’iyyar na jihohi sun bukaci ya yi karin bayani kan hakan, ko kuma su dakatar da shi dungurungun.

Sun bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da suka fitar, mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar Comrade Sunday Oginni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here