Uwargidan Tinubu, Shettima sun ziyarci Buhari a Daura

0
165

Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, a ranar Alhamis ta kai wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyarar ban girma a gidansa na Daura da ke jihar Katsina.

Uwargidan shugaban kasar wadda ta samu rakiyar uwargidan mataimakin shugaban kasa Hajiya Nana Shettima ta ce, sun kai ziyarar ne domin duba tsohon shugaban kasar, dubi da yadda ya dauke so tamkar ‘ya’yanshi.

Uwargidan shugaban kasar, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Busola Kukoyi, ya fitar, ta yi addu’ar Allah ya kara wa Buhari lafiya, ya kuma kara masa nisan kwana don goyon baya ga gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma ci gaba da taimaka wa Nijeriya baki daya.

A takaitaccen jawabin da ya yi bayan ziyarar, tsohon shugaban ya bayyana jin dadinsa, inda ya ce ziyarar da ta kai domin ganin yadda ya ke rayuwa bayan sauka daga mulki, ta bata mamaki.

Sauran wadanda suka samu rakiyar uwargidan shugaban kasar sun hada da uwargidan gwamnan jihar Katsina, Hajiya Dikko Radda da uwargidan shugaban majalisar dokokin jihar Katsina Hajiya Nasir Daura da sauran jiga-jigan mata na jam’iyyar APC a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here