Tinubu ya gana da El-Rufa’i da Wike a Aso Rock

0
147

Shugaban Kasa Bola Tinubu yanzu haka yana gana wa da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i da takwaransa na Ribas, Nyesom Wike a Fadar Shugaban da ke Abuja.

Tsofaffin Gwamnoni biyun dai na cikin mutanen da Shugaba Tinubu ya aike da sunansu ga Majalisar Dattijai da nufin nadawa Ministoci.

To sai dai majalisar ta ce an tabbatar da nadin Wike, amma na El-Rufa’i har yanzu akwai saura saboda wani rahoton tsaro da ake kokarin kammalawa.

Sun dai isa fadar ce ranar Laraba daban-daban.

Wike ne dai ya fara isa da misalin karfe 1:40 na rana, yayin da El-Rufa’i ya isa da karfe 2:00 na rana.

Majiyoyi a fadar sun ce tattaunawar ba za ta rasa nasaba da kokarin ganin majalisa ta tabbatar da nadin El-Rufa’in ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here