Abin da ya yi wa El-Rufai cikas wajen tabbatar da shi matsayin ministan Tinubu

0
148

Mallam Nasir El-rufa’i, tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma ɗaya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulki ya shiga halin ƙila-wa-ƙala a burinsa na sake zama minista.

Tsohon ministan Abujan, yana cikin mutum 48 da Majalisar Dattijan Najeriya ta tantance su a zaman kwanaki da ta yi, amma daga bisani ta jingine tabbatar da uku daga cikinsu a matsayin ministoci.

Wannan dai, wani babban koma-baya ne musamman ga Shugaba Bola Tinubu wanda ya ba da sunan ɗan siyasar kuma gogaggen ma’aikacin gwamnati, don naɗawa a sahun ministocinsa.

Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya ce ‘yan majalisar ba su tabbatar da Nasir El-rufa’i da Sani Abubakar Danladi daga jihar Taraba, da kuma Stella Okotete ta jihar Delta, har sai jami’an tsaro sun kammala tantance bayanansu.

Hakan dai yana nuna cewa, majalisar tana iya sake komawa kan batun kuma ta tabbatar da El-rufa’i, idan ta gamsu da tantancewar jami’an tsaro.

Sanarwar rashin tabbatar da El-rufa’i matsayin minista, ya zo da matuƙar ban mamaki ga ‘yan Najeriya, ganin wata uku kacal da ɗan siyasar ya kammala aiki a matsayin gwamnan Kaduna har wa’adi biyu.

A ranar Litinin 31 ga watan Yuli ne, majalisar ta katse hutunta inda ta koma aiki don tantance mutanen da ke Tinubu ke son naɗawa ministoci ciki har da El-rufa’i.

Bayan kammala aikin tantance sabbin minitocin da tabbatar da su a ranar Litinin, majalisar ta tafi hutun da ta fara, inda ake sa ran sai cikin watan Satumba, kafin ta sake komawa bakin aiki.

Don haka mai yiwuwa ne Shugaba Tinubu zai rantsar da majalisar ministocinsa ba tare da Nasir El-rufa’i ba, aƙalla da farko.

Nan da kowane lokaci ne, Bola Ahmed Tinubu zai rantsar da ministocin da majalisar ta tabbatar su 45 da kuma tura su ma’aikatun da za su fara aiki gadan-gadan.

Duk da haka, idan daga bisani Majalisar Dattijai ta tabbatar da shi minista, ana ganin tsohon ministan na Abuja zai iya samun wata hamshaƙiyar ma’aikata kuma ya kasance jigo a gwamnatin Tinubu.

Me ya faru lokacin tantance El-rufa’i?

Da ya bayyana a zauren majalisar dattijai ranar Talata, 1 ga watan Agusta, don tantancewa, tsohon gwamnan bai fuskanci wasu tsauraran tambayoyi daga ƴan majalisar ba.

Hasali ma yana cikin mutanen da majalisar ta ce tana nuna wa sanayya saboda kasancewarsa ɗan siyasar da ya taɓa riƙe muƙamin gwamna da kuma minista.

Majalisar ta ma hana sauraren wani ƙorafi da aka gabatar a kan Mallam Nasir El-rufa’i, bayan ya kammala karanta tarihin rayuwarsa da gwagwarmayar neman ilmi da na siyasarsa.

Wani ɗan majalisar dattijai, Sanata Sunday Karimi ne ya ja hankalin takwarorinsa game da ƙorafin da aka gabatar a kan El-rufa’i, wanda ya ce an bi ƙa’idar majalisar wajen gabatar da shi, sai dai shugaban majalisar ya ce an gabatar da ƙorafe-ƙorafe a kan mutane da dama waɗanda suka bayyana don a tantance su, amma bai saurari irin wannan ƙorafi ba.

Maimakon haka ya ce ana iya tura irin wannan ƙorafi zuwa fadar shugaban ƙasa da kuma jami’an tsaro don bin diddigi.

Haka zalika, rahotanni a baya-bayan nan sun ambato wata ƙungiya mai suna Gamayyar Mahaddata Al-Kur’ani da ita ma, take nuna jayayya da yunƙurin naɗa El-Rufai minista.

“Muna kira ga Shugaba Tinubu kada ya naɗa ƴan siyasar da ke taɓo a jikinsu,” jaridar Daily Trust ta ambato Gamayyar na cewa.

A cewarta, tana sukar naɗa El-Rufai minista ne bisa muradin zaman lafiya da kuma ci gaban ƙasa, ganin yadda yake adawa da tsarin karatun almajiranci.

Cikin ‘yan majalisa ƙalilan da suka yi wa El-rufa’i tambayoyi akwai Sanata Abdul’aziz Yari wanda ya nemi sanin abin da tsohon gwamnan na Kaduna zai yi don inganta samar da lantarki a Najeriya, idan mai yiwuwa ya zama ministan lantarki.

Da yake bayar da amsa, El-Rufai ya ce Najeriya tana da ƙarfin iya samar da lantarki tare da rarraba shi ga jama’a.

Ya ce dole a samar da sabbin kamfanonin raba lantarki a Najeriya, don kuwa daga kamfani 11 da ke wannan aiki a yanzu, uku ne kacal suke iya tafiyar da aikinsu yadda ya kamata.

Tsohon gwamnan ya ce aikin gyara ɓangaren lantarki a Najeriya, abu ne da zai buƙaci haɗin gwiwar kowanne ɓangare.

Tun lokacin da yake yaƙin neman zaɓensa, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta yi alfaharin yin aiki da mutane masu gogewa da ɗumbin ƙwarewa da tsinkaye kamar El-rufa’i.

Wane ne El-Rufai?

An haifi Malam Nasiru El-Rufai ranar 16 ga watan Fabrairun 1960 a jihar Katsina. Ya halarci Kwalejin Barewa, daga nan bayan kammala Sakandire, sai ya zarce zuwa Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, inda ya yi digirinsa na farko.

Ya kammala digirinsa na biyu a fannin gudanar da kasuwanci a 1984. A 2008 kuma sai ya tafi Birtaniya inda ya sake yin wani digiri a ɓangaren shari’a.

An naɗa shi a matsayin ministan babban birnin tarayya Abuja daga 2003-2007.

A lokacin ne ya jagoranci gagarumin aikin mayar da babban birnin na Abuja, kan taswirarsa ta asali, inda ya gudanar da aiki ba tare da nuna sani ko sabo ba.

Ya rushe gine-gine masu yawa waɗanda hukumomi suka ce an yi su ne ba bisa ƙa’ida ba. Kuma ya tabbatar da aiki bisa daidaita tsarin birnin, da kuma mayar da shi cikin hayyacinsa.

Haka kuma, irin ayyukan da El-Rufai ya yi a Abuja, ya sa ta shiga sahun birane mafi saurin ci gaba a duniya.

Ana yabonsa saboda ƙoƙarin da ya nuna wajen sake fasalin jihar Kaduna, inda ya yi mulki tsawon shekara takwas daga 2015.

Ya aiwatar da muhimman ayyukan raya ƙasa da bunƙasa harkokin ilmi, samar da ruwan sha da kuma gina gadoji da tituna.

Kuma duk da ƙalubalen tsaro da jihar ta sha fama da shi sakamakon hare-haren ‘yan fashin daji da rikice-rikicen ƙabilanci da na addini, masu sharhi na cewa El-rufa’i ya yi namijin ƙoƙarin wajen jan hankalin masu zuba jari a ciki da wajen Najeriya zuwa jihar Kaduna.

A tsawon shekarun mulkinsa, an ga yadda kamfanoni masu dama suka buɗe rassansu a cikin jihar.

Ana sukarsa saboda kasancewarsa ɗan siyasa mai yawan janyo taƙaddama, kuma a zamaninsa ne sojoji suka yi wa ‘yan shi’a dirar mikiya a Zariya a 2015, wanda daga bisani wata hukumar bincike da gwamnati ta kafa ta ce arangamar ta yi sanadin kashe mutum 349.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here